Cikin wani lamari Mai kama da Arashi, Adai – lokacin da jagoran jam, iyyar NNPP yake ta Sakin bayanai masu cin Karo da juna akafaf Yada Labarai da kafar sadarwa ta zamani wato (social media) yana nuni da cewar ko zai shiga jam, iyyar Apc Sai da wasu Alkawarurruka ko Kuma kwakykyawar makoma, mai lagwada, ko ma hanga Mai romo Sai ga Abokin fafatawarsa a siyasance, Rt Hon Alhassan Ado Doguwa Zababben Wakilin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa a majalisar kasa, ya karbi Daruruwan yayan jam, iyyar NNPP wadanda suka dangwarar da shahadarsu, suka karbi ta jam, iyyar Apc.

Wannan ana iya cewa wadannan matasa Maza da Mata dake yankin karamar hukumar Tudun wada sun yi nuni da cewar sun yi gaba kafin madugun ya yanke hukunci Kamar yadda jagoran Matasan malam Usman ranawa Dalawa ya bayyana a yayin da aka karbesu.

 

Usman Ranawa yace sunsheka babuwaya, sun jira jiran gawon shanu babu Hamza babu godiyar Hamza ma, ana dai anci Gari dasu babu romon Dimukradiyya. 

A saboda haka nema suka ce Dan lada akayin Sallah, suka fice daga jam, iyyar NNPP duk da kasancewar itace ke mulkin Jihar kano da karamar hukumar Tudun wada.

Da yake jawabi yayin karbar tsofaffin Yan jam, iyyar NNPP, Hon Doguwa ya yi Bayanin cewar jam, iyyar Apc ce jirgin fiton AL, umma itace jam, iyyar da ke kulawa da Baza romon Dimukradiyya a fai-fai kowa ya dauka ba tare da kyamaba.

Tuni dai tsofaffin yayan jam, iyyar NNPP sukayi jifa  da jajayen hulunan da suka zo dasu. Kana sukasha Aradun baiwa marada kunya tare da Aiki tukuru Dan samun Nasarar jam, iyyar Apc a ciki da wajen karamar hukumar Tudun wada.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version