JAMI, IN TSARO NA NSCDC YA RASA RANSA
jami’in Tsaro na Civil Defence ya rasa ransa yayin da yake kokarin kare jama’a a lokacin da wasu ‘yan daba suka kai hari a wani taron rabon tallafi.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Hon Hon Alhassan Ado Doguwa ke kaddamar da rabon tallafin shinkafa da kuma kudade kimanin naira miliyan 20 ga al’umma.
A yayin gudanar da taron ne wasu matasa da ake zargi ‘yan daba ne suka kai farmaki tare da yunkurin sace kudaden.
Hadimin Dan majalisar kan yada labarai Auwal Ali Sufi yace maharan sun yi nasarar kwashe kimanin naira miliyan 5 da dari daya, kafin jami’an tsaro su dauki matakin dakile su.
An ce jami’in na NSCDC ya rasa ransa ne a yayin kokarinsa na kare jama’a da dukiyoyinsu daga harin maharan.
Ya kuma jajantawa iyalan jami’in da ya rasu da kuma daukacin hukumar NSCDC bisa wannan babban rashi..
#viral #kano#jigawa#katsina#trending#community #facebookreel #community#highlight#kaduna
