A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.Wata Babbar Kotun Tarayya a Nijeriya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Ministan Shari’a na ƙasar Abubakar Malami da ɗansa da kuma wata mata kan Naira miliyan 500 da kuma mutane biyu da za su tsaya musu.
Alkali Emeka Nwite wanda ya bayar da belin ranar Laraba ya ce dole masu tsaya wa tsohon ministan su kasance sun mallaki kadarori a unguwannin Asokoro da Maitama da kuma Gwarinpa a Abuja sannan dole su miƙa fasfo ɗinsu ga kotu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa mutanen uku za su ci gaba da zama a gidan yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.
Kazalika an ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Fabrairu 2026.
Tsohon ministan da ɗansa da kuma matar suna fuskantar tuhume-tuhume 16 da suka haɗa halatta kuɗaɗen haramun.

