Rahotanni dake kan kafafen sadarwa na nuni da cewar, Tsohon mataimakin kwamishinan yansanda Abba kyari ya shaki iskar Yan,ci

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin kan zarge-zarge 23 da ake masa da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (NDLEA) ta shigar a kansa.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ta yi watsi tare da wanke muƙaddashin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari daga tuhumar da hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta yi masa, na ƙin bayyana kadarorin da ya mallaka.

 

Mai shari’a James Omotosho ya ce hukumar NDLEA ta gaza gabatar da ƙwararan shaidun ko kuma hujjoji da zai tabbatar da zargin da ake yiwa Kyari.

Mai shari’ar ya kuma bayyana zargin a matsayin na cin zarafi tare da yin watsi da ƙarar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version