
Mataimakin shugaban kungiyar masu gidajen bulo da dangoginsa ta kasa Shiyyar Arewa maso Yamma Alh Umar faruk musa shine yayi wannan Bayanin a Abuja, yayin taron da suka yi da hukumar dake kula da Ingancin Kayayyaki ta kasa (SON) ALH Umar faruk musa, yace Babu shakka Akwai bukatar su hada hannu da gwamnatin Jihar wajen bunkasa ayyukan kungiyar ta fuska Daban – daban domin raguwar zaman kashe wando a tsakanin matasa.
Haka zalika kakakin kungiyar reshen Jihar kano, Alh Nasir Mai bulo sharada, yayi Karin haske a bisa Ayyukan da Gwamnan Jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya Ke gudanarwa.
Alh Nasir Mai bulo na wannan batunne
Alokacinda da ya Ke bada rahoton sakamakon taron da suka gabatar a Abuja da hukumar kula da Ingancin Kayayyaki ta kasa (SON).
ALH Nasir mai bulo yace Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya biya Yan fansho, ya samar da ayyukan raya kasa wadanda suke da jibi da Sana, ar bulo, idan akayi duba da irin ayyukan da ya fitar a Jihar kano da makarantu da zai samar nan gaba bbu shakka ansamu karuwar Arziki da cigaban AL, umma,
A saboda haka nema Alh Nasir Mai bulo yake bayyana goyan bayan kungiyar ga Ayyukan raya kasa da Gwamnan Jihar Kano Alh Abdullahi Abba Kabir Yusuf ya Ke gudanar wa a sako da lungunnan Jihar kano.
Ita dai wannan kungiyar ta masu saida bulo da dangoginsa ta jihar Kano tana da mambobi akalla dubu 50 da shida, dake fadin jihar Kano