shugaban Yan Gwagwarmaya na Gidan Sanata Barau I Jibrin, kwamared Adamu Abdullahi karkasara ya bayyana Sanata Barau I Jibrin da cewar ya zama zakaran gwajin dafi a siyasar Nijeriya, bisa la’akari da kwarewarsa da yadda ya jajirce Bai yi kasa a gwiwa ba ya shiga Jami, ar Maryam Abacha ya yi karatun digiri na uku.

Karkasara ya ce duk da kasancewar sa mutum na biyu a majalisar Dattawa, kuma mataimakin shugaban majalisar Tattalin arzikin kasashen ECOWAS, wannan baisa ya gazaba Sai himma da DSP BARAU ya Kara wajen neman Ilimi.

Adamu karkasara ya Kara da cewar Akwai bukatar Yan siyasar wannan zamani suyi koyi da sanata Barau, duk da haka wannan na kunshe cikin sanarwar Taya Dr Sanata Barau I Jibrin murnar kammala wannan karatun digiri na uku Wanda hakan yayi nuni da irin kwazon da Dr, Barau I Jibrin yake dashi.

Hon Adamu Abdullahi karkasara ya yi Kari da cewar tun daga yankin Arewacin Nijeriya da Nijeriyar gaba daya Kwara babu Kumar Dr, Barau i Jibrin wajen kawo mahimman ayyukan raya kasa da cigaba domin ya kawo Jami, ar open University da polytechnic a yankin kano ta Arewa da Jami, ar koyar da Aikin noma ta Danbatta, baya ga romon Dimukradiyya da tuni yayi nisa wajen bazashi kowa ya samu

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version