Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken zargin kafa Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) ba tare da sahalewar doka ba, ya gayyaci Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) da kuma Ministan Harkokin Waje.
. Kwamitin ya ce ana son jami’an su bayyana yadda ake zargin majalisar ta gudanar da ayyukanta duk da tambayoyin da ake yi kan sahihancin kafuwarta da matsayinta a ƙarƙashin doka.
. Binciken na daga cikin ƙoƙarin Majalisar Wakilai na gano gaskiyar lamarin da kuma tantance ko an bi ƙa’idojin doka wajen gudanar da ayyukan PFIPC.
