Tun kafin a saka wasa Sai da magoya bayan kungiyar Kwallon kafa ta katsina united suka kawo hayaniya, abinda yasa ba, a saka wasan Akan lokaciba, ba, a saka wasa ba Sai karfe 04:30 na yamma.
Bayan ansaka wasanne kungiyar Kwallon kafa ta katsina united ta sanya Kwallo a ragar Barau FC.
Ba,, adade ba kungiyar Kwallon kafa ta Barau ta farke Kwallon wasa yadawo danye shakaf, nan take magoya bayan kungiyar Kwallon kafa ta katsina united suka tada hankali suka tada husuma a filin.
Tun da farko kafin kungiyar Kwallon kafa ta Barau FC ta farke Kwallon Sai da aka baiwa daya daga cikin Yan wasan Kwallon Kafa ta katsina united aka bashi Jan Kati, saboda rashin da, a
Alkalin wasa bai tashi ba Sai da ya Kara mintuna 10, kasancewar magoya bayan katsina Sun tada hankali a filin wasan,kana suka yiwa Yan wasan Barau FC munanan raunuka abin babu kyan gani a yanzu haka dai ana jiran Hukuncin da hukumar Kwallon Kafa ta kasa zata yi Akan wannan lamari.
Tuni dai katsina united suka yi kunnen doki Marar ci a yayin da suka zo wasa Jihar kano, da suka Je Jihar katsina akayi 1-1.
Wadanda aka jiwa rauni kuwa Yan wasan Barau FC sune Mai lamba 10 Abdurrazak Nana, da jabir da Abubakar shehu Dan, Auta da, Jabir Hassan kana aka yiwa motocin Barau FC rose, yayin da sauran Yan wasan suka Sha da kyar.
Haka abin yake idan akayi wasa tsakanin kano pillars da katsina united.
