Yayinda Babban zabe na shekara ta 2027 ke karatowa, matasan karamar hukumar kumbotso na cigaba da yin Damara wajen nuna akidarsu a bayyane kuma a siyasance,domin kuwa Al, ummar Kumbotso musanman matasa na cigaba da kai caffa da nuna goyan baya ga mai neman kujerar Majalisar kasa a inuwar jam, iyyar ADC a yankin karamar hukumar kumbotso Hom Hassan Ilyasu.

Hon Hassan Ilyasu ya karbi bakuncin dubban matasa masu kishin karamar hukumar kumbotso,da suka bukaci ya kawo cigbaa a yanki kamar aikin hanya da ya tashi daga karshen kwalta har zuwa Babban titin ring road.

Tun a shekarun baya yakamata ace anyi titin amma yagagara,bisa yadda aka samu takun saka tsakanin Tsohon shugaban karamar hukumar kumbotso da Tsohon wakilin karamar hukumar kumbotso a majalisar kasa rt Hon mannir Babba Dan, A gundi da Hon Hassan Garba farawa.

Rqshin aikin titin ya jawo wa yankin koma baya,a saboda haka nema matasan suka bukaci Hon Hassan Ilyasu da zarar ya dare kan kujerar Majalisar kasa,zai kai dauki gabarar cigaba da aikin Hanya da Taimakawa mata masu juna biyu da Dattawa da sauran Al, ummar yankin.

Hassan Ilyasu matashi ne dake kan gaba wajen kawo sauyi a siyasar yankin karamar hukumar kumbotso.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version