Allah ya yi wa fitaccen attajirin nan na Nijeriya kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP Alhaji Bamanga Tukur rasuwa yana da shekaru 90.

Iyalen marigayin sun shaida wa TRT Afirka cewa ya rasu ne ranar Asabar a gidansa da ke Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ana sa ran za a yi jana’izarsa a ranar Asabar din nan a Fadar Lamidon Adamawa, da ke Jihar Adamawa. Marigayin ɗan kasuwar, ya rasu ya bar ‘ya’ya 17.

Bamanga Tukur ya yi ministan masana’antu a lokacin gwamnatin Sani Abacha, sannan ya taɓa neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version