Gwamnatin Tarayya ta ware kusan Naira biliyan 9 da Miliyan 300 domin bukatun tafiye-tafiye da na abinci ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a cikin kasafin kuɗin shekara ta 2026, kamar yadda ke kunshe cikin bayanin da Ofishin Kasafin Kuɗi na Ƙasa ya fitar.

A cewar bayanan, Shugaba Tinubu shi kaɗai zai kashe kimanin Naira Biliyan 6.14 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen ƙetare, kazalika zai kasha Naira Miliyan 873.89 a tafiye-tafiyen cikin gida. Har ila yau, an ware Naira miliyan 431.62 domin abinci, da kuma kwalam da makwalashe a fadar shugaban ƙasa.

Shima ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, an ware masa Naira Biliyan 1.73 domin tafiye-tafiye da kuma Naira miliyan 186 62do min abinci, da kuma kwalam da makwalashe.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version