PCACC TA KAMA WANI BISA ZARGIN SAYAR DA GIDAN DAWAKIN GWAMNATI BA BISA KA’IDA BA A KANO
Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta sanar da kama wani mai suna Tasiu Adamu Maje, bisa zargin sayarwa da kuma bayar da hayar wani gidan dawakin da mallakin gwamnatin jihar Kano ne da ke filin tseren dawaki, wanda aka fi sani da Filin Sukuwa.
An kama wanda ake zargin ne bayan hukumar ta fara bincike sakamakon korafe-korafen da Muhammad Amir Yunusa da Usman Bala Yakasai (Sharif) suka shigar, inda suka zargi wanda ake zargin da miƙa tare da bayar da kadarar ga wasu mutane masu zaman kansu ba tare da samun izinin da doka ta tanada ba.
Binciken da PCACC ta gudanar ya gano cewa an gudanar da waɗannan mu’amaloli ne ba tare da sanin ko amincewar Hukumar Wasanni ta Jihar Kano (Kano State Sports Commission) ba, wadda ita ce hukuma da doka ta ɗora wa alhakin rabawa da kula da gidajen dawaki a jihar.
Abubuwan da Binciken Ya Gano
A yayin gudanar da binciken, hukumar ta gayyaci tare da tattaunawa da wasu daga cikin mutanen da ke da alaƙa da lamarin. Binciken ya gano cewa:
Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ba ta da masaniya kuma ba ta bayar da izinin wata mu’amala da ta shafi gidan dawakin ba.
Ba a taɓa ware gidan dawakin a hukumance ga wani mutum ba, ko ta hanyar sayarwa ko bayar da haya.
Takardar da wanda ake zargin ya dogara da ita wajen gudanar da mu’amalar ba ta kasance takardar da Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta amince da ita ko ta sani ba.
An kuma yi zargin cewa an yi amfani da wannan takarda da ba a amince da ita ba wajen gudanar da mu’amala da mutane biyu daban.
Sayarwa, bayar da haya ko miƙa gidan dawakin gwamnati ga mutane masu zaman kansu ba tare da samun amincewar da ake buƙata ba, ya saɓa wa manufofin gwamnati da ƙa’idojin gudanar da harkokin gwamnati.
Ana zargin Tasiu Adamu Maje ya amince ya sayar da gidan dawakin ga Muhammad Amir Yunusa kan kuɗi har Naira miliyan 4.5, yayin da a lokaci guda yake karɓar kuɗin haya daga Usman Bala Yakasai naira 180,000, inda aka ruwaito cewa an biya Naira 150,000 daga cikin kuɗin.
PCACC Ta Ce Mu’amalolin Ba Su Da Inganci
Bayan kammala binciken, hukumar PCACC ta bayyana cewa mu’amalolin da aka yi kan gidan dawakin ba su da izini kuma ba su da ingancin doka.
Hukumar ta ce kadarar har yanzu mallakin Gwamnatin Jihar Kano ce, kuma tana ƙarƙashin kulawa da gudanarwar Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.
PCACC ta jaddada cewa babu wani mutum da ke da ikon sayarwa, bayar da haya, miƙawa ko kuma yin wata mu’amala da kadarar gwamnati ba tare da samun izinin doka da na hukumomin da abin ya shafa ba.
Za A Kwato Kadarar, A Gurfanar da Wanda Ake Zargi
Hukumar ta ce tana ɗaukar matakan da suka dace domin kwato gidan dawakin tare da mayar da shi ƙarƙashin kulawar Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.
Ana kuma sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ke da hurumin sauraron shari’ar, inda za a ba shi damar kare kansa bisa tsarin shari’a.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da ɗaukar dukkan matakan gudanarwa da na shari’a da suka dace bisa tanadin doka.
Gargaɗi Ga Jama’a
PCACC ta gargadi duk mutanen da ke ƙoƙarin mayar da kadarorin gwamnati mallakarsu ko amfani da su wajen samun riba ta kashin kansu da cewa ba za ta amince da irin wannan ɗabi’a ba.
Hukumar ta ce kadarorin gwamnati ba na sayarwa ba ne ga mutane masu zaman kansu, kuma ba za a bayar da su haya ko amfani da su domin amfanin kashin kai ba tare da izinin da doka ta tanada ba.
Ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da binciken zarge-zargen da suka shafi karkatarwa, miƙawa ko mayar da kadarorin gwamnati hanyar kasuwanci ba bisa ka’ida ba, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan kafin shiga kowace irin mu’amala da kadarorin gwamnati.
PCACC ta ce masu son sayen fili ko gida, masu haya da masu zuba jari ya kamata su tabbatar da mallakar kadarar, yadda aka ware ta da kuma matsayin ta na doka kai tsaye daga hukumar gwamnati da abin ya shafa kafin su biya kuɗi ko shiga wata yarjejeniya.
PCACC Ta Jaddada Kare Kadarorin Jama’a
Hukumar ta sake jaddada aniyarta ta kare kadarorin gwamnati, hana amfani da dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba, da kuma inganta riƙon amana, gaskiya da kuma gudanar da albarkatun jama’a yadda ya kamata.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani zargin cin hanci da rashawa, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, karkatar da kadarorin gwamnati da sauran munanan ɗabi’u ta hanyoyin da hukumar ta tanada.
Related Posts
Add A Comment
