JIHAR JIGAWA TA KULLA YARJEJENIYAR DALA MILIYAN 10 DA WANI KAMFANIN INDIYA DON GINA KATAFAREN GIDAN KYANKYASAR KAJI
Gwamnatin Jihar Jigawa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta dala miliyan 10 da kamfanin Srinivasa Farms Private Limited na ƙasar Indiya, domin kafa katafaren gidan kyankyasar ƙwai na zamani a jihar.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sauya fasalin harkokin noma da bunƙasa kiwon kaji, inda ake sa ran sabon gidan kyankyasar zai kasance na farko mai irin wannan zamani a Arewacin Najeriya.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda ya jagoranci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wani muhimmin mataki wajen bunƙasa harkokin noma a jihar, yana mai cewa zai buɗe sabbin damarmaki ga masu kiwon kaji.
Gwamnan ya ce:
“Ina da yakinin cewa wannan aikin zai kawo sauyi mai girma a harkar kiwon kaji, ba kawai a Jihar Jigawa da Arewacin Najeriya ba, har ma da faɗin ƙasar baki ɗaya. Haka kuma, wannan na daga cikin ƙoƙarinmu na tallafa wa shirin gwamnatin tarayya na tabbatar da wadatar abinci.”
Malam Umar Namadi ya bayyana cewa an cimma wannan haɗin gwiwa ne bayan tattaunawa da kamfanin Srinivasa Farms, ciki har da ziyarar da tawagar gwamnatin jihar ta kai cibiyoyin kamfanin a Indiya, inda suka duba yadda ake gudanar da harkokin kiwon kaji da shirye-shiryen tallafa wa ƙananan manoma.
Ya ce yadda kamfanin ke ƙarfafa ƙananan manoma, tare da taimaka musu wajen bunƙasa kasuwancinsu da samar da sana’o’in da za su iya dorewa, ya burge tawagar jihar matuƙa.
Gwamnan ya ƙara da cewa:
“Mun yi imanin cewa Jihar Jigawa tana da masu kiwon kaji da dama waɗanda suka shafe shekaru suna fama da ƙalubale iri-iri, tare da fuskantar asara a harkokinsu.
“Ta hanyar wannan haɗin gwiwa, ina da yakinin cewa harkar kiwon kaji za ta bunƙasa a Jihar Jigawa, in Allah Ya yarda.”
Yarjejeniyar ta ƙunshi tanade-tanaden horaswa, ba da shawarwarin ƙwararru da taimakon fasaha, da sauran nau’o’in tallafi domin taimaka wa ƙananan masu kiwon kaji wajen inganta yadda suke kiwo da gudanar da harkokinsu na kasuwanci.
Gwamnan ya bayyana cewa yarjejeniyar gidan kyankyasar kajin na ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin haɗin gwiwa guda biyar da ake biɗa bayan ziyarar da ya kai ƙasar Indiya, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na jawo masu zuba jari, ƙarfafa sarƙoƙin samar da kayayyakin noma da samar da damarmaki ga matasa.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Kamfanin Srinivasa Farms, Mista Senthil Kumar Krishnan, ya ce haɗin gwiwar za ta mayar da hankali wajen ƙarfafa al’ummomin karkara da inganta ingancin samar da kaji ta hanyar amfani da fasaha da samar da kayayyaki masu inganci.
Ya bayyana cewa a halin yanzu, manoman Jihar Jigawa suna dogaro da sayen ƙananan kajin da aka ƙyanƙyashe kwana ɗaya daga wurare masu nisa, ciki har da Kaduna. Wannan doguwar tafiya na iya shafar lafiyar kajin kafin su isa hannun manoma.
Mista Senthil Kumar Krishnan ya ce:
“Ta hanyar samar da waɗannan ƙananan kaji a cikin gida, za mu iya magance waɗannan ƙalubalen. Za mu yi aiki tare da gwamnati domin samar da tallafin da ya dace ga manoma, ta yadda za su riƙa samun kaji masu inganci a lokacin da suke buƙata.
“Baya ga samar da kajin, za mu kuma ba manoma tallafin fasaha, tare da jagorantar su kan yadda za su kula da kajin domin samun sakamako mai kyau. Inganta yadda ake kiwo zai taimaka wajen ƙara ribar da manoma ke samu. Wannan shi ne babban burinmu.”
Haka kuma, Kwamishinan Bunƙasa Kiwo na Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, ya bayyana cewa wannan zuba jari zai taimaka wajen magance wasu manyan matsalolin da masu kiwon kaji ke fuskanta, musamman tsadar ƙananan kajin da kuma rashin tabbas wajen samunsu.
Ya bayyana cewa yawancin ƙananan kajin da ake samarwa manoma a yankin Arewa ana ɗauko su ne daga cibiyoyin samar da kaji da ke kudancin Najeriya, inda ake yin tafiyar da ta kai kimanin kilomita 1,200 zuwa 1,500.
Ya ce: “Irin wannan doguwar tafiya tana shafar yanayin lafiyar kajin, tare da rage saurin amsawarsu ga abinci.”
Farfesa Salim ya ce kafa gidan kyankyasar kajin a Jihar Jigawa zai rage nisan da ake tafiya wajen jigilar kajin sosai, inda ake sa ran babu wani wuri a jihar da zai kasance fiye da kimanin kilomita 150 daga cibiyar.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta tsara kafa wuraren rarraba kajin, tare da shigar da matasa cikin harkokin jigilar da rarraba ƙananan kajin da aka ƙyanƙyashe kwana ɗaya.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta nuna aniyarta ta samar da wani shirin tallafi da zai rage wa manoma nauyin kuɗaɗen da suke kashewa yayin gudanar da harkokin kiwo.
Kwamishinan Bunƙasa Kiwo na Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar, yayin da Mista Senthil Kumar Krishnan ya sanya hannu a madadin kamfanin Srinivasa Farms Private Limited na ƙasar India
Related Posts
Add A Comment
