Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya Yi Jimamin Rasuwar Sani Lawan Kofar Mata.

Hon Alhassan Ado ya bayyana alhininsa tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan, ‘yan uwa, abokan arziki da daukacin al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, tsohon Darakta-Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano.

Wata sanarwa da mai magana da yawun  Hon Alhassan Ado Doguwa, Auwal Ali Sufi utai,ya fitar ranar Lahadi, ta bayyana cewa , Hon Alhassan Ado ya ce rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata babban rashi ne ga Jihar Kano.
Doguwa Wanda shine shugaban Yan majalisun Arewacin nijeriya ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen aikin gwamnati da kuma inganta jin dadin al’umma, musamman a harkokin kula da aikin Hajji da walwalar maniyyata.
Ado Doguwa ya ce za a ci gaba da tunawa da marigayin bisa irin hidimar da ya yi wa Jihar Kano da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa tsarin kula da jin dadin alhazai.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya jikansa, Ya ba shi madaukakin matsayi a Jannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa, abokansa da daukacin al’ummar Kano hakurin jure wannan babban rashi.

Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON Rt Hon Alhassan Ado Doguwa yayiwa iyalan marigayin nasiha  da su yi hakuri tare da tuna cewa mutuwa kaddara ce da babu makawa ga kowane mai rai, yana mai addu’ar Allah Ya saka wa marigayin da alheri bisa hidimar da ya yi wa al’umma.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version