Rundunar ’yansandan Jihar Neja ta tabbatar da gano wani bam da bai fashe ba a ƙauyen Zugurma da ke ƙaramar hukumar Mashegu, a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna ranar Talata, inda ya ce an gano nakiyar ne bayan wani rahoto da ofishin ’yansanda na Ibbi ya samu daga mazauna yankin da suka ga wani abin da suka zarga da bam a cikin daji.
Abiodun ya ce jami’an ’yansanda sun isa wurin cikin gaggawa, suka killace yankin don tabbatar da tsaro, yayin da sashen kwance bamabamai na rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Mohammed Mamun ya gudanar da aikin kwance bam ɗin cikin nasara. An mika shi zuwa hedikwatar ’yansanda da ke Minna, inda ake ci gaba da bincike domin gano asalin sa. Kwamishinan ’yansandan jihar, Adamu Elleman, ya bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da aiki don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
