Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Ahmed Sanusi ya sanar da kama jami’an na su da suka aikata laifin waɗanda ya ce ba su da dalilin ci gaba da zama a cikin aikin saboda ɓarayi ne.
Sanusi ya ce jami’an sun kafa shinge ba bisa ƙa’ida ba, a kusa da Banex dake unguwar Wuse, inda suka tare shugaban ICPC Dr Musa Aliyu, kuma su ka tuhume shi da laifi, kana suka tilasta masa ciro naira dubu 53,000 a POS domin ba su cin hanci.
