Kwamishinan dake kula da AL, amuran majalisar kasa, Hon yusuf A Yusuf Tabuka Gwarzo ya bayyana Sanata Barau I Jibrin da cewar mutum ne da ya dace ya rike kowanne irin Mukamin a siyasar kasannan bisa la, akari da kwarewarsa ta fanni daban – daban.

Hon yusuf Tabuka na wannan bayaninne acikin sakon Taya murna ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa na kasa Kuma mataimakin shugaban Majalisar kasashen ECOWAS Sanata Barau I Jibrin CFR, PhD, Fcn bisa kammala karatun digirin digirgir (PHD) a fannin kasuwancin masana, antu a Jami, ar Maryam Abacha

Wannan na nuni da irin jajircewarsa da kokarinsa da sanya karsashi ga manyan gobe domin su yi koyi da halayyarsa ta neman Ilimi Dan cigaban kasa baki daya.

 

 

Ina taya Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin, CFR, PhD, FCNA, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Mataimakin Shugaban Majalisar ECOWAS, murna bisa nasarar kammala karatunsa na digirin digirgir (PhD) a fannin Kasuwancin Kamfanoni a Jami’ar Maryam Abacha.

Kwamishinan hukumar dake kula da AL, amuran majalisar kasa ya taya Hon Hon Dr Barau I Jibrin murnar kammala wannan karatu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version