Tinubu Ya Shiga Ganawa Ta Sirri da Alhassan Doguwa a Villa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a halin yanzu yana wata ganawa ta sirri da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Doguwa/Tudun Wada a Jihar Kano, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja.
Wakilinmu ya lura da zuwan Doguwa a hanyar da ta nufi ofishin Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 7:15 na dare, kimanin mintuna 20 bayan da aka ga Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Gboyega Oyetola, ya isa harabar fadar shugaban ƙasar.
Ziyarar Oyetola na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan magajinsa, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta.
A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya isa farfajiyar ofishin Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 6:12 na yamma, yayin da Ministan Yaɗa Labarai ya riga ya kasance cikin ofishin yana ganawa da Shugaban Ƙasa a lokacin da Akpabio ya isa.
Haka kuma, an ga Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Dele Alake, a fadar shugaban ƙasar cikin wannan lokaci. Ana kyautata zaton ziyararsa na da alaƙa da taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka tsara gudanarwa a ranar Laraba.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ajandar ko abin da aka tattauna a waɗannan taruka daban-daban ba.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ware ranar 19 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar fara kamfen ɗin siyasa a hukumance gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
