wani jami’in gwamnatin Uba Sani ya yi murabus
Babban Mashawarci na Musamman ga gwamnan jihar Kaduna kan samar da ababen more rayuwa (Counselor on Infrastructure) Malam Samaila Abdu Suleiman, ya yi murabus daga muƙaminsa a yau Litinin, ba tare da bada ƙwaƙwarar dalilin ɗaukan wannan matakin ba.
Sai dai cikin takardar yin murabus ɗin da ya aika zuwa ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Sama’ila ya ce ya ajiye mukamin ne domin maida hankali kan harkokinsa wanda hakan ya yi daidai da tsarin doka, inda ya miƙa godiya ga gwamnan jihar Malam Uba Sani.
Me ku ke gani a matsayin dalilin da ya sa manyan jami’an gwamnatin Kaduna ke yin murabus a baya-bayan nan?
Shigo Shafin Jaridar 👉 muryar Arewa Ayau. Com domin samun labarai
