Wani SSR Ɗin Gwamna ya tozarta Dan Jarida A Gaban Manyan Jami’an Gwamnatin Kano

‎Wani dan jarida daga Jihar Kano ya bayyana shirin kai kara kotu biyo bayan zargin cin mutuncinsa da wani jami’in gwamnatin jihar ya yi a yayin gudanar da bakin tsaren motoci a wani bangare na gasar Kamun kifi da ake gudanarwa a garin Argungu dake Jihar Kebbi.

‎Lamarin ya faru ne a filin tseren mota na Kano, a cikin taron da aka shirya domin bikin cika shekara 61 na wannan shahararriyar gasa.

‎Jami’in da ake zargi shi ne Auwal Sani Rogo, SSR na Gwamnatin Jihar Kano, yayin da dan jaridar da abin ya shafa shi ne Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai, wanda ke gudanar da aikin sa matsayin sa na kwararren Dan Jarida.

‎Shaidu sun bayyana cewa cin mutuncin ya faru ne bayan Sharifai da wasu ‘yan jarida sun yi hira da masu halarta a wurin.

Lamarin ya faru ne a gaban manyan jami’an gwamnati ciki har da ‎Ibrahim Abdullahi Waiya, kwamishinan yada labarai da harkokin Cikin Gida da Bayani da ‎Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, kwamishinar Harkokin Al’adu da Yawon Bude Ido da kuma ‎Alhaji Abba El-Mustapha, shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano.

‎Bayan faruwar lamarin, Sharifai ya shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Bompai, sai dai Rogo bai amsa kiran ‘yan sanda ba, yana amfani da Gidan Gwamnatin Jihar Kano a matsayin kariya daga kama shi.

‎Kwamishinan Waiya ya gayyaci dan jaridar domin tattaunawa, inda ya yi alkawarin shiga tsakani domin nemawa Rogo afuwa.

Sai dai har yanzu babu wani bayani ko neman afuwa daga Rogo ko gwamnatin Jihar Kano, ko ofishin mashawarci na musamman ga gwamnan Abba Kabir Yusuf.

‎Majiyoyi kusa da Sharifai sun ce idan har ba a dauki mataki ba, kai kara kotu na iya zama hanya mafi dacewa domin kare hakkin sa da mutuncin aikin jarida.

‎Lamarin yana ci gaba da jawo muhawara a tsakanin ‘yan jarida a Kano kan girmama aikin jarida da ‘yan jaridu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version