Wasu fusatattun mabiya sun yi wa dan majalisar tarayya na Dawakin Tofa, Tofa da Rimingado a Kano sun yi wa ɗan majalisarsu na tarayya Hon. Tijjani Abdulƙadir Joɓe ihun ba ma yi a taron zaɓen shugabannin jamʼiyya.
Arewa ta rawaito daga jawabin da makusancin ɗan majalisar Auwal Galadima Jemomi ya wallafa cewa yana tsaka da jawabi a garin Tofa, sai wani daga baya ya soma magana cewa, “wallahi mai gida akwai gyara, mu mafarauta ba ka duba mu ba” daga nan ne sai ɗan majalisar ya miƙa abin magana a salo na galatsi cewa to zo ka yi bayani.
Baya ga nan a wasu bidiyoyi da alʼummar garin Tofa suka ɗauka waɗanda suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna yadda ake koƙarin tseratar da ɗan majalisar da gudu a mota.
A gefe guda fusatattun mabiya na ci gaba da ihu har ma da masu zage-zage.
Ko a farkon wannan wata na Fabrairu da mu ke ciki, Dan Majalisar ya roƙi alʼummar da ya ke wakilta su yi wa Allah da maʼaika su yafe masa a yayin taron masu ruwa da tsakin jamʼiyyar, taron da aka tashi dutse a hannun riga.
Kujerar DTR na fuskantar ƙalubale laʼakari da jiga-jigan jamʼiyyar da suka rufe ido wajen neman kujerar.
