Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 13, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, ta bayar da umarnin tsare lauya Barrister Dalhatu Shehu Usman a gidan yarin Kurmawa har zuwa ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da lauyan bisa zargin almundahana, ƙirƙirar rasit na bogi da kuma ƙin halartar zaman kotu.

A zaman kotun na yau, lauyan wanda ake tuhuma, Barrister A.A. Sani, ya ƙalubalanci hurumin lauyoyin da za su gurfanar da wanda yake karewa, yana mai cewa ba su da ikon gudanar da shari’ar.

Ya kuma roƙi kotun da ta tura wanda yake karewa gidan yari maimakon mayar da shi hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, inda ya shafe sama da kwanaki 10 bisa umarnin kotu.

Kotun ta ɗage sauraron batun zuwa ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, domin yanke hukunci na wucin gadi kan ƙalubalen hurumin lauyoyin, tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan yarin Kurmawa har zuwa wannan rana.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version