fKotu ta bada belin shugaban kungiyar Miyetti Allah,  Bodejo kan Naira biliyan 2

 

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin  shugaban kungiyar Miyetti Allah Kauta Hore, Bello Bodejo, kan Naira biliyan 2 bisa zargin da ake masa na halasta kuɗaɗen haram.

 

Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci Bodejo ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, kowannensu da darajar belin Naira biliyan 2. Daya daga cikinsu dole ne ya gabatar da takardar biyan haraji ta shekara uku kuma ya kasance mazaunin Abuja, yayin da ɗayan kuma dole ne ya mallaki fili mai darajar Naira biliyan 2 a Abuja.

 

Kotun ta kuma umarci Bodejo ya miƙa fasfo ɗinsa na fita ƙasashen waje ga rajistar kotu, tare da hana shi fita daga Najeriya sai da izinin kotu.

 

Alƙalin ya ce laifukan da ake tuhumarsa da su na da damar beli, sannan ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoba domin fara shari’a. Bodejo ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da Hukumar EFCC ta gabatar a kansa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version