Hasashen siyasar wannan zamani na nuni da cewar Rt Hon eng Muhammad Ali wudil FNSE shine mutumin da ya riki kujerar majalisar wakilai ta tarayya, yayin da ya Kai mahimman ayyukan raya kasa, Wanda babu wanda ya taba aiwatar da irin sa a yankin kananan hukumomin wudil da Garko.

A gudanar da  Ayyukan raya kasa  A dukkan mazabun kananan hukumomin wudil da Garko Wanda a yanzu haka babu irin wadannan ayyukan.

Hausawa kance ta Yaro kyau take Bata karko, kwarewa da sanin makamar aiki ya sanya Rt Hon eng Muhammad Ali wudil ya Samarda aikin hanyar data tashi tun daga wudil Asibiti ta biyo utai, har zuwa Darki da iyakar Jihar kano da jigawa, iya wannan aikin kadai ya tabbatar wa Mai hankali cewar, an yi zaben tumun dare a siyasar wannan yankin, domin har yanzu babu project irin wannan a yankın wudil da Garko.

Uwa uba ma samar da gidan wuta na Lantarki, wannan kadai shaidane ne domin kuwa makiyan cigaban yankin kananan hukumomin wudil da Garko sun San eng Muhammad Ali wudil FNSE yayi aikin da Yaro ba zai iya ba. Kuma Bai yi ba.

Marayu da na kasassu sun San irin gudummawar da eng Muhammad Ali wudil ya bayar, balle Yan Makaranta da suka Amfana da tallafin karatu.

Jaridar muryar Arewa Ayau. Com a wani bincike data aiwatar ta rawaito cewar Wannan ayyukan kadan Kenan baya ga masallatai da Dattawan Gari da aka mutunta da Mata da matasa da suka Amfana da romon Dimukradiyya daga Rt Hon eng Muhammad Ali wudil FNSE

Yanzu dai ya rage hankalin Mai yankan kaba ya koma ga rina, al, ummar wudil da Garko kuyi wa kanku kiyamullaili kada ku sake Bari ayi muku sabatta juyatta bisa la, akari da fadawa Hannun Yan sari da suka gaza wajen kawo cigaban yankın kanananan hukumomin wudil da Garko

 

 

Gidan wuta na wudil da yake bada Hasken Wutar Lantarki kadan daga cikin Ayyukan eng Muhammad Ali wudil FNSE.

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version