An wayi gari da ganin gagarumin yawan jami’an tsaro a ciki da wajen Fadar Gwamnatin Jihar Kano, biyo bayan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa tura jami’an tsaron ya biyo bayan tsananin adawa da shirin sauya sheƙar gwamnan ke fuskanta, musamman daga mambobin ƙungiyar Kwankwasiyya da magoya bayansa a faɗin jihar.

Wata majiya daga bangaren tsaro ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kauce wa duk wani rugujewar doka da oda a jihar ta Kano.

“Babu shakka wannan mataki ya fusata da dama daga cikin magoya bayan gwamnan da na tafiyar Kwankwasiyya. A halin yanzu, gwamnan ba ya jin daɗi a kan lamarin,” in ji majiyar.
Binciken DAILY NIGERIAN, hakan ya nuna cewa an killace dukkanin hanyoyin shiga da fita na Gidan Gwamnati da jami’an tsaro.

A ranar Juma’a, DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa gwamnan ya kammala shirye-shiryen sanar da sauya sheƙar sa zuwa APC a ranar Litinin. Sai dai daga bisani an ɗage shirin sakamakon tsananin adawa daga mazauna jihar Kano da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.

Majiyoyi sun ce an ɗage matakin ne domin bai wa gwamnan damar yin ƙarin shawarwari da shugabannin APC, tare da ƙoƙarin janyo goyon bayan ‘yan Majalisar Tarayya da na Majalisar Dokokin Jihar Kano domin marawa shirin sauya shekar baya.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma uban siyasar gwamnan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesanta kansa da shirin sauya sheƙar a fili.

Da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana shirin a matsayin cin amanar ƙuri’ar jama’ar da suka zabi gwamnan karkashin jam’iyyar NNPP.

Har ila yau, Kwankwaso ya soki kiran da wasu zaɓaɓɓun shugabanni da masu mukami a gwamnatin jihar ke yi na buƙatar gwamnan ya jagorance su zuwa APC, yana mai bayyana hakan a matsayin abin dariya da rashin tunani.

A halin yanzu, magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya sun kara kaimi wajen shirye-shirye da hada-hadar siyasa, yayin da ake rade-radin ficewar gwamnan daga tafiyar.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta lura cewa ƙarin magana ta Hausa wato “A ci dadi lafiya”, wadda ke nufin “a more rayuwa cikin salama”, ta zama taken da magoya bayan Kwankwasiyya ke amfani da shi wajen sukar gwamnan da masu mara masa biyayya

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version