Shugaban Yan majalisun Arewacin nijeriya rt Hon Alhassan Ado Doguwa Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON, ya baiwa makarantar Alfawa,iq kyautar Naira MILIYAN guda, yayinda Daliban makarantar da Suka yi saukar karatun Alqur ani Maigirma su 32. Ya basu Naira Dubu Dari uku da Ashirin.
RT Hon Alhassan Ado Doguwa ya ja hankalin Al, ummar jihar kano da au kasance masu taimakawa makarantun Alqur, ani dana Islamiyya domin bunkasa ilimin Addinin musulunci a tsakanin matasa.
RT Hon Alhassan Ado ya ce ana samun gurbacewar tarbiyya ne sakamakon rashin ilimin Addinin musulunci, a saboda haka nema ya kalublnci Iyaye da su zage Damtse wajen baiwa yara tarbiyya tare da Ilimin Addini dana zamani domin samun shugabanni Nagari.
RT Hon Alhassan Ado Doguwa Wanda yayi jawabi akan yadda Allah Madaukakin Sarki ya halicci Dan Adam,domin ya bauta masa kana yace bautar bazata ta yiwuba har sai Annemi ililimim sanin ALLAH,
Tun da farko sai da shugaban makarantar Islamiyya Alfawa, iq IBarr,Ishaq Adam Ishaq, ya bayyana rt Hon Alhassan Ado Doguwa da cewar shugabane abin koyi kuma yana daga cikin yan majalisun Arewacin nijeriya da suke kwato hakkin Al, ummar su a majalisar kasa.
Bar Ishaq Adam Ishaq ya ce bazai manta da gudummawar da rt Hon Alhassan Ado ya bayar a majalisar kasa,akan harkokin tsaro,harma ya shaidaswa shugabannnin nijeriya gaskiya akan harkokin tsaro.
Barr Ishaq Adam Ishaq ya godewa RT HON ALHASSAN ADO DOGUWA bisa halartar saukar karatun Alqur ani da kuma kyautar kudade kimanin Naira MILIYAN guda da DUBU Dari uku da Ashirin da ya baiwa makarantar da Daliban
RT Hon Alhassan Ado Doguwa ya yabawa Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Hon murtala sule Garo bisa yunkurin su na inganta ilimi a jihar kano.
Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu bisa yunkurin sa na ciyar da kasa gaba ta fuskar Ililmi
