Shugaban Yan majalisun Arewacin nijeriya rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya ja hankalin Daliban da ke karatu a manyan makarantu da su tabbatar sun zabi shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu a karo na biyu a matsayin shugaban kasa.
Rt Hon Alhassan Ado na bayyana cewar shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu ya bujiro da sabbin munufofi domin Inganta ilimi tun daga tushe.
Abinda ya kama tun daga gyaran makarntu zuwa sabon tsarin Tallafawa Dalibai na Nelfund domin cigaban Ilimi.
A saboda haka nema Hon Alhassan Ado ya bukaci Daliban da su tabbatar sun zabi shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu a zaben shekara ta 2027.
Da ya juya game da gudummawar da ya baiwa Ilimi rt Hon Alhassan Ado ya bayyana cewar ya sayawa Daliban karamar hukumar Doguwa gida sukutum dake makwbtaka da kwalejin Ilimi ta Sa adatu Rimi baya ga baiwa Daliban Tallafin karatu.
Ko a makon da ya gabata rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya samarda ajujuwan Dalibai masu yawa a mazabu Daban -Daban na yankin kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa.,Baya ga Nasarar da ya samu na gina Ajujuwan Dalibai a dukkan mazabun Kannan hukumomin Tudun wada da Doguwa a lokacin da yake rike da shugabancin kwamitin cimma muradun karni MDG

Tuni dai kungiyar Daliban ta DOLSA ta karrama Hon Alhassan Ado Doguwa da lambar yabo bisa yadda ya ke gudanar da Ayyukan raya kasa da cigaban Dalibai.
Yayinda RT Hon Alhassan Ado Doguwa Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON ya sayi kalandar Daliban akan kudi kimanin Naira MILIYAN 2.
.
