Al, ummar yankin sheka karshenkwalta,sun koka bisa yadda ma,aikatar kasa da safiyo ta jihar kano tayi fatali da aikin Hanyar data tashi daga sheka karshen kwalta zuwa wailari.
Al, ummar yankin sunyi kira ga Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da ya kafa kwamitin da zai bi diddigin aikin Hanyar tun lokacin Gwamna Malam Ibrahim shekarau,
Haka zalika Al, ummar sun koka yadda aka bayyana cewar ba a biya su kudin Diyyyar Gidajen su da aka rushe ba.
Yayinda Tsohon shugaban karamar hukumar kumbotso Alh Hassan Garba farawa da Tsohon Danmajalisar Tarayya mai wakiltar kumbotso a majalisar kasa Alh munnir Babba Dan Agundi suka gaza wajen gudanar da aikin Hanyar Duk da kasancewar Hon mannir Babba ya yi aiki daga karshen kwalta zuwa Gadar Dantsinke,bai kammala aikn Hanyar ba,

Wani abu mai kama da wasan yara lokacin da Hon mannir Babba Dan Agundi yayi yunkurin fara aikin kwatsam sai akace karamar hukumar kumbotso ta ce itace zatayi,ga aikin nan iya na Hon mannir ne babu na Hon Hasaan Garban kauye farawa,in banda rudu da ya sanya mutane a ciki na rashin tabbas.

Tun da farko Gwamnatin jihar kano ta baiwa kamfanin Kimpex aikin kuma anyi Kashi 60 bisa dari domin anyi gadoji da kwalbart gefe da gefe.

Tun daga knupda zuwa ma aikatar kasa da safiyo Al, umma yankin sheka sun yi bibiya baya ga kiraye kiraye da sukayi a kafafen yada labarai da na sadarwa na zamani, Amma shiru malam yaci shirwa

A yanzu haka daga gadar Dantsinke iyakar aikin da Hon mannir Babba Dan Agundi yayi zuwa gidan Dinya zuwa wailari,mata da kananan yara da masu juna biyu sun shiga uku bisa yadda hanyar bata biyuwa cikin dadin rai,hatta Wanda ke tafiya a kasa ma kokawa yake saboda rashin kyauwun hanyar.

Al, ummar yankin na kira ga Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da taimakawa Dubban Al, ummar yankin a kammala aikin Hanyar  kasancewar Hanyace da zata bulle zuwa Na,ibawa flay over kuma zata Bunkasa Tattalin ARZIKIN Al’ummar yankin da jihar kano baki daya.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version