APC TA JIHAR JIGAWA TA KADDAMAR DA KWAMITIN YAƘIN NEMAN ƘURI’U NA 2027, TA ƘARA JADDADA GOYON BAYANTA GA TINUBU DA NAMADI
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Jigawa ta ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Ƙuri’un Shugaban Ƙasa da na Gwamna na zaɓen shekarar 2027, inda Gwamna Malam Umar Namadi ya zama Shugaban kwamitin, yayin da Alhaji Lawan Ya’u Roni aka naɗa a matsayin Darakta-Janar.
Ƙaddamar da kwamitin ya haɗa manyan shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa ƙarƙashin tsari guda, domin daidaita harkokin wayar da kai da tattara goyon bayan al’umma ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Umar Namadi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamitin na da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman; tsohon Gwamna, Barrista Ali Sa’adu Birnin Kudu; tsohon Gwamna, Sanata Ibrahim Saminu Turaki; da Shugaban APC na jihar, Hon. Ahmad Garba MK, a matsayin mataimakan shugabannin kwamitin.
Sauran manyan jami’an kwamitin sun haɗa da Sanata Muhammad Ibrahim da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, waɗanda aka naɗa mataimakan shugabanni na shiyyar Arewa maso Gabas ta ɗaya da ta biyu.
Haka kuma, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin da Hon. Farouk Adamu Aliyu su ne mataimakan shugabanni na shiyyar Kudu maso Yamma ta ɗaya da ta biyu, yayin da Alhaji Isa Gerawa da Hajiya Rabi Ishaq suka samu muƙaman mataimakan shugabanni na shiyyar Arewa maso Yamma ta ɗaya da ta biyu.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da kwamitin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna a ƙarƙashin tsari guda na da manufar ƙarfafa haɗin kai da daidaita ayyukan jam’iyyar, tare da samar da dandali guda na gudanar da yaƙin neman zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana farin cikinsa bisa yadda jama’a da dama suka halarci taron, yana mai cewa hakan ya nuna ƙarfin APC da yadda jam’iyyar ke da gagarumar kasancewa a faɗin Jihar Jigawa.
Ya ce taron ya ƙara masa kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC a shirye take ta samu nasara a dukkan matakan zaɓen da ke tafe.
Gwamna Namadi ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta da su haɗa kai wajen tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sake zaɓensa a matsayin gwamnan jihar, da kuma samun nasarar ‘yan takarar APC a majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin Jihar Jigawa.
A kalamansa, gwamnan ya ce:
“Da ikon Allah, muna da cikakken yaƙinin cewa za mu samar da nasara ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Gwamna, sanatocinmu, mambobin majalisar wakilai da kuma mambobin majalisar dokokin jiha.”
Haka kuma, Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Jihar Jigawa za ta cika burin samar da ƙuri’u miliyan biyu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya ƙara da cewa, “Idan aka yi la’akari da abubuwan da muka gani a yau, muna da yakinin cewa za mu samar da waɗannan ƙuri’u ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Insha Allah.”
A nasa jawabin, tsoffin gwamnonin Jihar Jigawa guda biyu, Barrista Ali Sa’adu Birnin Kudu da Sanata Ibrahim Saminu Turaki, sun yaba wa Gwamna Namadi bisa nasarorin da ya samu wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa da suka shafi rayuwar al’umma, tare da bunƙasa jihar cikin ƙasa da shekaru huɗu da fara mulkinsa.
Sun bayyana cewa nasarorin gwamnan za su zama babbar dama ga jam’iyyar APC a lokacin yaƙin neman zaɓe, tare da ƙara mata damar samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Barrista Ali Sa’adu Birnin Kudu ya bayyana Gwamna Namadi a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa irin ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar sun rage wa masu suka damar samun abin faɗa a kansa.
A cewarsa:
“A yau a Jigawa, kowa ya amince cewa Gwamna Namadi mutum ne mai gaskiya. Babu wanda zai iya tuhumarsa kan rashin riƙon amana ko zargin sa da almundahana da kuɗaɗen al’umma. Duk wanda ya faɗi wani abu marar kyau a kansa, to ya yi hakan ne saboda hassada, ƙiyayya ko kishi, domin babu wani abin zargi a kansa.”
Shi ma Sanata Ibrahim Saminu Turaki ya bayyana Gwamna Namadi a matsayin shugaba mai adalci, bin ƙa’ida da tausayi, yana mai cewa gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen bunƙasa ababen more rayuwa da harkar ilimi a jihar.
Sanata Turaki ya yi tsokaci musamman kan ci gaban da aka samu a fannin hanyoyi a faɗin jihar, da kuma ɗaukar dubban malamai aiki, inda ya ce ba a taɓa samun irin wannan ɗaukar malamai ba tun bayan lokacin da yake kan mulki.
Ya ce:
“Shin akwai wata jiha a Najeriya a yau da za ta iya nuna kyakkyawan tsarin hanyoyi da ya kai na Jihar Jigawa? Tun bayan da na bar mulki, ba a sake ɗaukar malamai aiki ba. Akwai wasu makarantu da suka rufe saboda ƙarancin malamai. Wane ne a yau ya ɗauki dubban malamai aiki kamar yadda Gwamna Namadi ya yi
