Wata sanarwa da ta fito daga bakin Babban Mai Taimakawa DSP sanata Barau I jibrin akan kafafen yada labarai kwamared Adamu Abdullahi Karkasara, yabayyana cewar, mataimakin shugaban majalisar Dattawan ya gana da kungiyoyin matasa da mata da yan Gwagwarmaya da ke Dabbaka tafiyar sanatan a yankin kano ta Arewa domin baza romon Dimukradiyya suma su amfana.
Daga ciki wadanda suka gana da sanata Barau I jibrin sun hada da yan Akwati tun daga tushe , kowacce karamar hukuma daga cikin guda 13 dake karkashin ikon DSP ta samu Baburan hawa fiye da 140 .da injinan Taliya da kekunan Dinka da injinan markade da miliyoyin kudade.
Yayinda sanata Barau I jibrin ya gana da kungiyoyin matasa yan Gwagwarmaya na kafafen yada labarai ,kano first Media Group Karkashin jagorancin Alhajiji Nagoda,
Yayinda sanata Barau ya basu kimanin naira miliyan 20 Baburan hawa guda 20 mota 1 tare da Alkawarin Duk wata DSP zai Bada naira miliyan 5 har zuwa lokacin zabe na shekara ta 2027,domin karfafa musu gwiwa tare da Tallata jam, iyyar APC.
Karkasara ya ce sanata Barau I jibrin ya gana da yan media na yankin kano ta Arewa masu tallata manufofi, yayinda ya Gwangwaje su da kudi kimanin naira miliyan 10 da mota da Baburan hawa guda 6.
DSP sanata mai wakiltar kano ta Arewa ya yi ganawa ta musanman da masu kare kima da muhibbar sanatan a kafafen yada labarai na ciki da wajen jihar kano da suka hada da kafafen sada zumunta, yayinda ya basu Naira miliyan 20 da mota da Baburan hawa ,hade da Alkawarin bada wasu makudan kudade duk watan Duniya har akammala zabe.
Wannan shine kadan daga cikin romon dimukradiyya da sanata Barau I jibrin ya yi wa magoya bayan sa,duk da haka banda Dunkuli na karfafa gwiwa da yake yiwa masoyan nasa masu tallata haja da kare kima da muradan sa.
