Sanata Abdulkarim Abdussalam Wanda aka fi Sani da AA ZAURA,, yayin da ya cika shekaru 49 a rayuwa yana hidimtawa Al’umma, ta fuskar Addini da tattalin arziki, da zaman takewa.
Wani Babban AL, amari da Abdussalam Abdulkarim AA ZAURA yake dashi shine mutum ne mai tasay, da yakana da sanin yakamata,.
Mafiya yawan Abokan huldarsa sunyi masa shedar sada zumunci da Hakuri da kyauta da taimakawa na kasa da jinkai.
Ko a kwanakin nan ya Samarda motocin daukar marasa lafiya da motocin kashe gobara da motar gidan marayu dan Kai su makaranta baya ga shirye – shiryen fada karawa da ilimintarwa a kafafen Yada Labarai, ga kyaututtukan dake sanya Dalibai kwazo wajen neman Ilimin Addini dana zamani Kamar yadda Mai magana da yawun Sanata AA Zaura, Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu ya bayyana wa jaridar, Muryar Arewa Ayau. Com.
Acikin shekaru 49 Sanata Abdulkarim Abdussalam AA ZAURA ya taimakawa Addinin musulunci.
Ayyukan raya kasa, kuwa sun hada da gina ofishin Yan Sanda a yankin karamar hukumar ungogo domin kare rayukan da dukiyoyin AL, umma, kana ya Gina makarantun Islamiyya da dama a Jihar kano,Kamar yadda Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu Ya bayyana.
Fatan mu shine Allah ya Karo shekaru Albarka a rayuwa.
