An Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina Kan Zargin Lalata Allunan Siyasa

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro biyu da ke kula da tsaron Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wato Aide-de-Camp (ADC), Hassan Bello, da Chief Security Officer (CSO), suna tsare a hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ke Abuja tun ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an tsaron biyu suna hannun jami’an tsaro a Abuja, yayin da aka ce Chief of Staff na Gwamnan Katsina, Alhaji Abdulkadir Nasir, ya je Abuja domin neman a sake su, amma ƙoƙarinsa bai yi nasara ba, kamar yadda jaridar Katsina Times ta rawaito.

Haka kuma, wata majiya ta ce Gwamna Dikko Radda da kansa ya yi ƙoƙarin ganin an saki jami’an tsaron nasa, sai dai har zuwa yanzu ba a samu nasarar sakin su ba.

An ce an tsare jami’an ne sakamakon zargin hannu a lalata wasu manyan allunan talla da ke kan hanyar daga Modoji Roundabout zuwa Gidan Gwamnatin Katsina.

Wasu daga cikin allunan na ɗauke da hotunan Gwamna Radda, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da wasu fitattun ’yan siyasa.

Rahotanni sun ce an lalata wasu daga cikin allunan, musamman waɗanda ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabir Masari.

Bayan faruwar lamarin, an kai ƙorafi ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar DSS, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka fara gudanar da bincike.

A yayin binciken, an kama wani mutum da ake zargin jagoran wata ƙungiyar siyasa ne a Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Aminu Nasta.

Majiyoyi sun ce bayan kama Aminu Nasta da kuma bayanan da aka samu yayin bincikensa, jami’an tsaro sun gayyaci ADC da CSO na Gwamna Radda domin yi musu tambayoyi.

Ana zargin jami’an tsaron biyu da kasancewa suna da masaniya kan lamarin, ko kuma sun taimaka wajen kare wasu daga cikin mutanen da ake zargi da lalata allunan da ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da Ibrahim Masari.

Sai dai, har yanzu ba a bayyana wata hujja a bainar jama’a da ke tabbatar da cewa jami’an biyu sun hannu kai tsaye wajen lalata allunan ba.

Lamarin ya sake jawo hankali kan rikicin siyasa da ake zargin yana ƙara tsananta tsakanin wasu ɓangarori a cikin jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, musamman tsakanin masu goyon bayan Gwamna Radda da ɓangaren da ake dangantawa da Ibrahim Masari da wasu manyan ’yan siyasa a Abuja.

Wasu ’yan siyasa na ganin cewa rikicin cikin gida na APC a Katsina na iya ƙara ɗaukar sabon salo yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, musamman idan aka fara amfani da hukumomin tsaro wajen magance rikicin siyasa.

Har yanzu dai akwai tambayoyi kan dalilin da ya sa aka tsare jami’an tsaron da ke kula da lafiyar Gwamnan Katsina, da kuma ko akwai wata hujja da ta tabbatar da alaƙarsu da lalata allunan kamfen.

Ana kuma kira ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su bayyana dalilin tsare ADC da CSO, tsawon lokacin da za a ci gaba da tsare su, da kuma irin laifin da ake bincikensu a kai.

Ci gaba da tsare jami’an biyu ya ƙara haifar da tambayoyi kan yadda rikicin siyasar APC a Katsina ke ƙara shiga cikin harkokin tsaro da gwamnatin jihar, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version