Hon Dahiru Ahmad Wanda ya Kai dauki ga yankin bisa yadda yaji wasu yan siyasa dake yawo da wani Dantakarar da bai wuce Dankoyo a siyasance ba, Wanda bai san hanyar majalisar kasa ba,balle ya kai kudiri.

Mai Huddadu yace yankin rano kibiya da Bunkure yankin rt Hon kabiru Alhassan Rurum ne, saboda ya gudanar da Ayyukan raya kasa da tarihi bazai manta da shiba.

Sakamakon mahimman Ayyukan raya kasa da samar da Aikin yi ga matasa da mata da manoma yasa mutanen yankin ke zabar rt Hon Alhassan Rurum,kuma babu Wanda zai zo yayi katsalandan akan harkokin siyasar Al, umma yankin bisa kaunar rt Hon Alhassan Rurum.

Mai Huddadu yace rt Hon kabiru Alhassan Rurum yazama shugaba a majalisar kasa, saboda haka nema ya ce kada su zabi sabon yanka rake da sai yayi sabon karatu a majalisar kasa.

.kada ku bari wani yayi muku dadin baki ku sake zabar rt Hon Kabir Alhassan Rurum domin cigban yankin kananan hukumomin Rano kibiya da Bunkure,shine jirgin fiton Talakawa.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version