Gwamnan Yobe Buni da Mai Bai wa Tinubu Shawara, Masari, Sun Ba Kungiyar Izala JIBWIS Naira Miliyan 600

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da babban mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, sun yi alkawarin bayar da jimillar Naira miliyan 600 domin tallafa wa aikin gina Jami’ar Fortune University ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS).

An sanar da alkawarin ne yayin wani taron JIBWIS da aka gudanar a Jos, inda Ibrahim Kabir Masari ya bayyana cewa zai bayar da Naira miliyan 300 domin tallafa wa aikin jami’ar.

A cewar rahoton Daily Trust, Masari ya kuma bayyana cewa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, shi ma ya yi alkawarin bayar da karin Naira miliyan 300, wanda ya sa jimillar kudin da aka yi alkawari ta kai Naira miliyan 600.

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wajen ganin an kammala aikin jami’ar.

Sheikh Jingir ya bayyana cewa jami’ar ba mallakinsa ba ce, yana mai cewa idan aka kammala ta, za ta kasance wata cibiyar ilimi da za ta amfani Musulmi da Kiristoci baki daya.

Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da tallafa wa aikin domin ganin an cimma manufar kafa jami’ar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version