Hon kawu Idris Hausawa ya bayyana cewar babu abinda ya’yan jam, iyyar APC suke bukata Illa a taimakesu da dukkan abinda ya kamata wadanda ke neman aiki abasu,da wadanda za,a tarfawa romon Dimukradiyya,domin kaiwa ga Gaci a kakar zabe mai zuwa.

Hon kawu Idris Hausawa na wannan bayaninne alokacin da ya ke gudanar da taron shekara -shekara Wanda ake gudanar wa a Gidauniya foundation dake kan Titin jami,ar Bayero dake kano.

..Taron da ya hada DUKKAN magoya bayan Hon kawu Idris Hausawa wanda ya hade kan dukkan gidajen siyasar yankin.

.Hon kawu Idris yace lokaci yayi da yansiyasar wannan zamani zasu daina tara kudi,su jibanci lamarin Al’umma domin kuwa shine kan gaba wajen sauke nauyin da aka dora musu..

Matasan wannan zamani suna nuna kauna ga jam, iyyar APC domin itace jam, iyyar mutanen jihar kano..

Lokaci yayi da Gwamnan jihar kano Abba.,zai dinke dukkan wata baraka a yankin karamar hukumar Gwale,inji Hon kawu Idris Hausawa.

Awajen wannan taron akwai maieneman kujerar sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim shekarau, ya yi Dogon bayani akan yadda, shugabanni yakamata su tallafawa,na kasa da su

Sanata shekarau ya sha aradun cewar, za,a samu Nasarar zabe mai zuwa Amma sai kowa ya sauke nauyinsa a jam,iyyance.

 

Wannan taro ya hada Masu ruwa da tsaki na jam, iyyar APC na karamar hukumar Gwale da tsantsar magoya bayan Hon kawu Idris Hausawa.

Da yake jawabi sakataren jam, iyyar APC na jihar kano Hon salis maje Ahmad Gwangwazo, ya bayyana cewar Apc tana bukatar sadaukar da kai da jajirce wa domin kai APC ga Nasara a Babban zabe mai zuwa.

Dubban matasan Yan GWGWARMAYA dake goyan bayan Hon kawu Idris Hausawa da kungiyoyin matasa da suka fito domin nuna goyan baya ga Hon kawu Idris Hausawa ne da tsoffin kwamishinoni da suka hada da Hon yakubu lawan yarima,da hon hajiya Binta Yarmulki da Tsohon shugaban karamar hukumar Gwale da tsoffin kansiloli da da Hon AA sule da, sauran matasa ne da mata suka halarci taron.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version