An tabbatar da Rt Hon Alhassan Ado Doguwa a matsayin Dantakara guda daya tilo da zai wakilci kananan hukumomin tudun wada da Doguwa takarar majalisar wakilai a Inuwar jam, iyyar Apc.

Kamar yadda Uwar jam, iyyar Apc ta kasa ta bada umarni cewar a gudanar da sulhu ko masalaha a dukkan kujerun da ake ganin an samu masu bukata da suka haura mutum guda, idan masalaha Bata yiwuba Sai ayi zabe Kato bayan Kato.
Wannan ce tasa jam, iyyar Apc ta turo wakilian ta domin suyi alkalanci bisa yadda tabbatar war take inganta.
Yayinda a gefe guda masu ruwa da tsaki da Wakilan hukumar zabe ta kasa, ke ganin yadda abin yake.
Haka ta kasance a yankin karamar hukumar Tudun wada, aka tara masu ruwa da tsaki da yayan jam, iyyar Apc na yankin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa da karkashin jagorancin Wakilin jam, iyyar Apc na Jihar kano kuma Mai bawa jam, iyyar Apc shawara ta fuskar shari, a, kuma Babban lauya Mai lambar kwarewa ta SAN Abdul Abdul fagge, Wanda ya tabbatar da Bayanin yayan jam, iyyar Apc da masu ruwa da tsaki da Dattawan jam, iyyar Apc sun Amince Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya cigaba kuma shine Dantkarar majalisar kasa a kakar zaben shekara ta 2027.

Haka akayi a Tudunwada haka akayi a Doguwa,
Yanzu dai babu tababa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa shine DA takarar majalisar kasa a kakar zaben 2027 a jam’iyyar APC, a yankin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version