GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA KADDAMAR DA KWAMITIN JAGORAN AIKI DOMIN AIKI DA ASUSUN CIGABAN RUKUNAN ZABE
I’m Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da Kwamitin Jagoranci na Jiha domin fara aiwatar da dokar Asusun Ci gaban Rukunin Zabe (Polling Units Development Funds), a wani muhimmin mataki na bunkasa cigaban al’umma a matakin kasa.
Da yake kaddamar da kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya taya mambobin kwamitin murnar nada su, tare da bayyana irin amincewar da Gwamna Malam Umar A. Namadi ya nuna gare su.
Ya bayyana cewa sabuwar dokar da aka samar na da manufar cike gibin da ke tsakanin manufofin gwamnati da kuma bukatun jama’a musamman a matakin karkara da mazabu.
Malam Bala Ibrahim ya ce aikin kwamitin shi ne bayar da jagoranci, tsare-tsare, sanya ido da kuma tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata a fadin jihar.
Sakataren gwamnatin ya kuma bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci da rikon amana tare da tabbatar da bai wa al’umma damar shiga cikin dukkan ayyukan ci gaba.
Da yake mayar da martani a madadin kwamitin, Shugaban Kwamitin, Honourable Ibrahim Garba Hannun-Giwa, ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa wannan dama da aka ba su ta yi wa al’umma hidima, tare da tabbatar da cewa za su gudanar da aikinsu bisa tanadin doka.
Mambobin kwamitin sun hada da:
Honourable Ibrahim Garba Hannun-Giwa – Shugaba
Honourable Gambo S. Malan – Mamba
Dr. Muhammad Hassan – Mamba
Shehu Kaila – Mamba
Garba Muhammad Dutse – Mamba
Abdullahi S.G. Shehu – Mamba
Sanata Mujitaba Mohammed – Mamba
Barrister Usman Adamu – Mamba
Ahmad Garba MK – Mamba
Sibu Abdullahi – Mamba
Adamu Muhammad GBS – Mamba
Muhammad Yusha’u – Sakatare
Wannan mataki na nuna kudirin gwamnatin Jihar Jigawa na tabbatar da gaskiya, rikon amana da shugabanci nagari domin inganta rayuwar al’ummar jihar.
