GWAMNA NAMADI YA YI ALHININ RASUWAR TSOHON DAN MAJALISAR TARAYYA, HON. ABBA ANAS ADAMU
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar alhini da jimamin rasuwar tsohon dan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Abba Anas Adamu, inda ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan halartar sallar jana’izar marigayin da aka gudanar a Kano ranar Talata, inda ya hada kai da ‘yan uwa, abokan siyasa, abokai da masu alhini wajen yi wa mamacin addu’ar samun rahama da gafara.
Gwamna Namadi ya bayyana marigayi Hon. Abba Anas Adamu a matsayin jajirtaccen mai hidimtawa al’umma wanda ya sadaukar da wani bangare mai muhimmanci na rayuwarsa wajen yi wa jama’arsa da bil’adama hidima.
Ya kuma ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban na aikin gwamnati, ciki har da kasancewarsa tsohon dan Majalisar Wakilai ta Tarayya, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Guri, tsohon Kwamishina a Jihar Jigawa, tare da kasancewarsa gogaggen malami a fannin ilimi.
Gwamnan ya ce za a ci gaba da tunawa da marigayin musamman saboda tawali’unsa, jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuradiyya, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen cigaban siyasar Jihar Jigawa.
A karshe, Gwamna Namadi ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansa, abokan arziki, abokan siyasa da daukacin al’ummar Jihar Jigawa hakurin jure wannan babban rashi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version