Muna kan Hanyar Sauya Filin Jirgin Sama na Dutse zuwa Cibiyar Jigilar Kaya – Gwamna Namadi
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa na kan turbar sauya Dutse International Airport zuwa cibiyar jigilar kaya (cargo hub).
Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta samu amincewa daga Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN) domin fara girka kayayyakin jigilar kaya a filin jirgin saman, a shirye-shiryen kaddamar da cikakken aikin filin jirgin kaya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da wata tawagar kwararru daga Nigerian Airspace Management Agency (NAMA) ta gudanar da duba kayayyaki da gwajin inganci (calibration) a filin jirgin.
Yayin da yake ganawa da tawagar NAMA, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin bin ka’idoji da nagartattun tsare-tsaren harkokin sufurin jiragen sama.
“Yau rana ce mai muhimmanci a kokarinmu na tabbatar da cewa dukkan kayayyakin filayen jirgin sama a Jihar Jigawa suna aiki daidai da mafi kyawun ka’idoji,” in ji gwamnan.
Ya kuma yabawa mahukuntan filin jirgin saman bisa yadda suke daukar matakan tsaro da muhimmanci ta hanyar gudanar da gwaje-gwajen daidaiton kayan aiki.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa tattaunawa da FAAN ta haifar da samun amincewar fara girka kayayyakin jigilar kaya a filin jirgin.
“Mun dade muna tattaunawa da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya, kuma sun ba mu amincewa domin fara girka kayayyakin jigilar kaya a filin jirgin, a shirye-shiryen kaddamar da cikakken filin jirgin kaya,” in ji shi.
Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da kiyaye ingantattun ka’idoji yayin da filin jirgin ke shirin zama daya daga cikin mafi kyau a Najeriya.
“Yau muna iya cewa da alfahari cewa wannan na daga cikin mafi kyawun filayen jirgin sama a Najeriya. Za mu ci gaba da rike wannan matsayi!”
Tun da fari, shugaban tawagar NAMA ya bayyana cewa zuwansu Dutse na da nufin duba kayan aikin jagorantar jiragen sama (navigational aids) tare da tabbatar da cewa suna aiki daidai da ka’idojin Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya, tare da gwada yadda kayan aikin ke aiki domin tabbatar da ingantaccen aiki baki daya.
