Gwamnatin Najeriya ta roki jama’a su rage cin ganda (ponmo) kada kamfanin sarrafa fata na kasar ya durkushe

Daga Jaridar Muryoyi

Gwamnatin Tarayya ta gargadi ‘yan kasa kan ci gaba da cin ganda (ponmo), tana cewa hakan na barazana ga masana’antar fata ta Najeriya wadda aka kashe fiye da dala biliyan 5 wajen ginawa.

#Muryoyi ta ruwaito Daraktan Cibiyar Bincike da Ci gaban Kayan Gado (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ne ya bayyana haka a taron kaddamar da yakin neman rage cin ponmo da aka gudanar a Abuja.

Ya ce ganda na da muhimmanci wajen samar da kayayyakin fata da ake fitarwa kasashen waje, amma yawancin su ana karkatar da su don abinci, wanda hakan ke rage ci gaban masana’antar.

Zaku rage cin ganda ko kuwa dama bakwa ci?

 

×

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version