Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu da nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu.

Wannan mataki ya fara aiki nan take.

Gwamnan ya umarci Alhaji Sagagi da ya mika ragamar ma’aikatar ga Babban Sakataren ma’aikatar.

Ana sa ran zai kammala mika ragamar aiki zuwa gobe da safe.

Gwamna Yusuf ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version