Cikin wata sanarwa da shugaban rukunin kamfanin fortuneRice mills Alh Dalhatu Shehu ya sanyawa hannu, wadda aka rabawa manema labarai, a Jihar kano, ta bayyana cewar
Hankalinmu ya kai kan wasu rahotanni da ke yawo a wasu kafafen yada labarai dangane da rufe kamfanin sarrafa shinkafar mu na fortune Rice mills dake rukunun masana’antu na Sharada da Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Kasa (NESREA) ta yi bisa zargin karya dokokin muhalli.
Duk da cewa mun amince da alhakin da NESREA ke da shi na tabbatar da bin ka’idojin muhalli, muna ganin ya dace mu fayyace wasu batutuwa domin a samu daidaitaccen bayani tare da kwantar wa jama’a, abokan hulɗarmu da kuma al’ummar da ke zaune a yankin hankali.
Da farko, kamfaninmu na fortune Rice ya kasance yana gudanar da ayyukansa bisa tsarin dokokin Najeriya tare da ci gaba da jajircewa wajen kiyaye ingantattun ka’idojin muhalli da masana’antu. A matsayinsa na kamfani mai kishin al’umma, mun bayar da gudunmawa sosai tsawon shekaru wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma inganta wadatar abinci a Jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.
Mun lura da koke-koken da aka gabatar dangane da ƙurar da ake zargin tana fita daga kamfanin, hakan baya nufin mun yi shakulatn bangaro da hanyoyin kiyaye wada lafiyar mazauna kusa da kamfanin ba, Sai dai yana da muhimmanci a bayyana cewa tuni kamfanin ya dauki matakai na gyara da inganta ayyukansa domin ƙara ingancin aiki tare da ƙarfafa tsarin kula da muhalli a cikin harabar masana’antar.
Saɓanin yadda Hukumar NESREA ke ƙoƙarin nuna lamarin, mahukuntan kamfanin ba su yi biris da tattaunawa da hukumomin ba, Mun ci gaba da kasancewa cikin hulɗa da hukumomin da abin ya shafa tare da nuna cikakken shirin ba da haɗin kai wajen magance duk wasu matsalolin da aka gano yayin bincike.
Haka kuma muna son tabbatar wa mazauna yankunan da ke kewaye da kamfanin cewa lafiyarsu, tsaronsu da walwalarsu na da matuƙar muhimmanci a gare mu. Kamfanin bai taɓa yin wani abu da gangan da zai iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari ko lalata muhalli ba.
A cikin fahimtar juna da haɗin kai, a halin yanzu muna aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙwararrun masana muhalli da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an warware duk sauran matsalolin bisa tanadin dokokin muhalli na ƙasa.
Saboda haka muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa yaɗa bayanan da ba su da sahihanci waɗanda za su iya haifar da rashin fahimta ko kuma bata sunan kamfani da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Kamfaninmu na fortune Rice zai ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan masana’antu cikin nagarta, kare muhalli da kuma zaman lafiya da al’ummomin da ke kewaye da shi.
Amadadin Shugaban kamfanin sarrafa Shinkafa na fortune Rice
Kwanakin nan ansamu takun saka tsakanin kamfanin fortune Rice mills da hukumar muhalli ta kasa
