Gwamna Namadi Ya Yi Taro da Kwararrun, daga Saudiyya Kan Bunƙasa Noman Dabino a Jigawa

 

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gudanar da wani muhimmin taron da wakilan Gidauniyar Dabino ta Ƙasar Saudiyya, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ahmad Al-Jabbar na Jami’ar King Fahad.
Taron wanda aka gudanar a gidan Jakadan Ƙasar Saudiyya da ke Kano, ya samu halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin; Darakta Janar na Hukumar Sauya Fasalin Noma ta Jihar Jigawa (JATA), Dr. Saifullahi Umar; da Darakta Janar na Cibiyar Bincike ta Jihar Jigawa, Dr. Sulaiman Rufa’i; tare da Jakadan Ƙasar Saudiyya.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin haɓaka noman dabino ta hanyar amfani da sabbin fasahohi na zamani, ciki har da fasahar rarraba kwayoyin halitta (molecular segregation) da kuma fasahar kiwon shuka a dakin gwaje-gwaje (tissue culture), domin inganta ingancin iri da ƙara yawan amfanin gona, ta hanyar cin gajiyar ƙwarewar Saudiyya a wannan fanni.
Gwamna Namadi ya bayyana jin daɗinsa kan damar tattaunawa da ƙwararrun Saudiyya wajen bunƙasa noman dabino a Jigawa, inda ya yaba da kyakkyawar dangantaka mai ɗorewa tsakanin Jihar Jigawa da Ƙasar Saudiyya, musamman a fannonin ilimi da noma. Ya kuma bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da gwamnatin jihar ke tattaunawa da abokan hulɗarta na Saudiyya kan shirin bunƙasa gonakin dabino.
Gwamnan ya ce bisa la’akari da yalwar ƙasar noma mai dacewa da noman dabino a Jigawa, jihar na ci gaba da kasancewa kan gaba a Najeriya wajen samar da dabino.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da cikakken bincike kan dukkan itatuwan dabino da ke fadin jihar, tare da shirye-shiryen kafa sabbin gonaki a wurare biyar daban-daban. Ya jaddada muhimmancin horas da manoma kan sabbin dabaru domin ƙara yawan amfanin gona.
A cewarsa, wannan shiri zai ƙara yawan amfanin gona, ya haɓaka kudaden shiga na manoma, tare da faɗaɗa damar fitar da dabino zuwa ƙasashen waje.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana cewa shirin na da nufin shuka sabbin tsirrai 10,000 na dabino, da suka haɗa da nau’ukan gida da na kasuwanci, tare da samar da cikakken horo ga matasa.
A halin yanzu, hekta 1,042 na ƙasa na ƙarƙashin noman dabino, wanda ke samar da aikin yi ga matasa 400, tare da shirin faɗaɗa damar zuwa matasa 1,000. A ƙarƙashin shirin, kowane matashi da ya shiga zai samu rabin hekta domin tallafa wa rayuwa mai ɗorewa da bunƙasa tattalin arziki ga kowa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version