Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Zartarwa Don Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Inganta Tarbiyyar Al’umma a Jigawa
Daga Dutse
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan wasu dokokin yaki da shan miyagun kwayoyi,zartarwa guda biyu da nufin ƙarfafa yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi tare da samar da ingantaccen tsari na wayar da kan al’umma da gyaran tarbiyya a faɗin jihar.
An gudanar da bikin sanya hannun kan dokokin ne a ranar Talata a zauren Majalisar Zartarwa da ke Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa a Dutse, inda aka kafa Kwamitin Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi na Jihar Jigawa da kuma shirin Wayar da Kan Al’umma da Gyaran Tarbiyya.
Bikin ya samu halartar Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (Mai Ritaya), manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an tsaro, ƙungiyoyin fararen hula da abokan hulɗar ci gaba.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa dokokin wani muhimmin mataki ne na cika alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka a cikin ajandar ta mai maki 12 da kuma jawabin rantsuwar kama aiki, musamman wajen haɗa kai da hukumomin tarayya domin magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi, ƙarfafa shugabanci a matakin ƙasa da kuma inganta ɗabi’u a cikin al’umma.
Ya ce dokokin za su samar da tsari guda ɗaya da zai haɗa rigakafi, jinya, gyaran hali, wayar da kan jama’a da kuma tallafa wa hukumomin tsaro wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi. Haka kuma za su ƙarfafa dabi’u na kishin ƙasa, gaskiya, ladabi, biyayya ga doka, ɗaukar alhakin ƙasa da kuma hidimar al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da suka faru bayan zanga-zangar watan Agustan 2024 sun nuna muhimmancin ɗaukar irin waɗannan matakai, yana mai cewa rashin aikin yi, yaɗuwar bayanan ƙarya da ƙarancin tarbiyya na iya sa matasa su faɗa cikin munanan halaye.
A cewarsa, ci gaba mai ɗorewa ba ya ta’allaka ne kawai kan aiwatar da ayyuka da shirye-shirye ba, har ma yana buƙatar al’umma mai ɗabi’a ta gari wadda ta ginu kan al’adunmu da koyarwar addinin Musulunci.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa matasan Jigawa na daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban jihar, amma ya yi gargadin cewa shan miyagun ƙwayoyi na iya lalata makomar su idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ya ce bai wa matasa dama ba tare da tarbiyya ba na iya jefa su cikin ɓata hanya, yayin da tarbiyya ba tare da damar samun ci gaba ba kan haifar da takaici. Don haka gwamnati za ta ci gaba da samar da damarmaki tare da inganta tarbiyya domin gina matasa masu kishin ƙasa da zaman lafiya.
Gwamnan ya ƙara da cewa sabbin dokokin sun zo ne domin ƙarfafa wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta riga ta fara aiwatarwa, ciki har da kwamitocin ci gaba na matakin gunduma da Asusun Ayyukan Raya Al’umma, domin ƙara ba jama’a damar shiga harkokin ci gaba da tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Ya jaddada cewa yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ba zai yi nasara ba sai an haɗa ƙarfi tsakanin jami’an tsaro, rigakafi, ba da shawara, gyaran hali, goyon bayan iyalai da kuma sa ido daga al’umma.
Gwamnan ya yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin addini da na gargajiya, ma’aikatu, ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin matasa da su ba da gudummawa wajen samar da shirye-shiryen koyon sana’o’i, kasuwanci, noma, fasahar zamani, wasanni, masana’antun ƙirƙira da kuma ayyukan ci gaban al’umma.
Ya yabawa Hukumar NDLEA bisa kyakkyawar haɗin gwiwar da take yi da gwamnatin Jigawa, tare da jinjinawa ofishin hukumar na jihar bisa nasarorin da ya samu, ciki har da kama kusan kilogram 2,000 na miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta haura naira biliyan 2.8, tare da samun hukuncin kotu kan mutum 136 da aka samu da laifi.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NDLEA ta Ƙasa, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya bayyana cewa babu wani gwamna a Najeriya da ke bai wa hukumar goyon baya kamar Gwamna Umar Namadi.
Ya ce gwamnan ya samar wa hukumar fili domin gina bariki na dindindin, ofisoshi, gidan kwamandan jihar da kuma sauran tallafin da ke ƙarfafa ayyukan hukumar a Jigawa.
Marwa ya yabawa Gwamna Namadi bisa kokarin da yake yi wajen sauya fasalin jihar, yana mai cewa shugabanci mai hangen nesa shi ne mafita ga matsalolin zamantakewa.
Ya kuma bayyana cewa daga Janairun 2021 zuwa Disamban 2025, NDLEA ta kama mutane 77,859, ta samu hukuncin kotu kan mutum 14,122, ta ƙwace kilogram miliyan 14.8 na miyagun ƙwayoyi, tare da yi wa sama da mutum 50,000 jinya da gyaran hali a cibiyoyinta da ke faɗin ƙasar.
A ƙarshe, Marwa ya ce yawan masu amfani da miyagun ƙwayoyi a Jigawa ya kai kusan kashi bakwai cikin ɗari, wanda ke daga cikin mafi ƙanƙanta a Najeriya, yana mai bayyana fatan cewa sabon Kwamitin Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi zai taimaka wajen ƙara rage wannan adadi ta hanyar rigakafi, wayar da kan jama’a da kuma ci gaba da haɗin gwiwa.
