Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dokta Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya  bayar da takin ZAMANI ga manoma. domin bunƙasa harkokin noma ta hanyar rabon takin zamani kyauta ga manoma.

A ci gaba da wannan ƙuduri, Gwamna Nasir Idris ya sayo tare da rabawa manoma takin zamani da ya kai tirela 110, ba tare da sun biya ko sisi ba. A halin yanzu, ana ci gaba da rabon takin a ƙananan hukumomi 21 na jihar domin tabbatar da cewa haƙiƙanin manoma ne suke cin gajiyar shirin.

An ƙaddamar da wannan shiri ne domin ƙara yawan amfanin gona, bunƙasa samar da abinci, inganta harkokin noma, da kuma tallafa wa dubban iyalan manoma a faɗin Jihar Kebbi.

Wannan mataki ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatin Gwamna Nasir Idris na ƙarfafa fannin noma, wanda shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Jihar Kebbi. Haka kuma, yana nuna manufar gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma tare da bai wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu wajen samun nasara.

Al’ummar jihar da dama na kallon wannan a matsayin wani gagarumin ci gaba da ga cikin manyan shirye-shiryen rabon takin zamani kyauta da aka taɓa aiwatarwa a tarihin Jihar Kebbi.

Jihar Kebbi na ci gaba da Bunkasa  harkar noma 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version