GWAMNATIN JIGAWA TA KULLA YARJEJENIYA DA STARAGRI WEST AFRICA DOMIN TALLAFA WA MANOMAN SHINKAFA 20,000
— Gwamna Namadi Ya Sanar da Tallafin Kashi 30 Cikin 100 Na Kayan Noma da Raba Famfunan Ruwan Hasken Rana 6,000 Ga Manoma
Gwamnatin Jihar Jigawa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin StarAgri West Africa Limited domin ƙara bunƙasa harkar noma da kuma tallafa wa ƙananan manoma a faɗin jihar.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta samar da kayan noma ga manoman shinkafa 20,000 da ke gudanar da noman rani, tare da ƙaddamar da wasu shirye-shiryen rage tsadar noma da ƙara ribar manoma.
Gwamna Malam Umar Namadi ne ya jagoranci bikin rattaba hannun da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse, tare da halartar jami’an kamfanin StarAgri West Africa Limited, ma’aikatar noma, ma’aikatar shari’a, JASCO da kuma mambobin kwamitin fasaha na harkokin noma na jihar.
A madadin kamfanin StarAgri West Africa Limited, shugabar kamfanin kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa shi, Misis Sandy Eyal ce ta sanya hannu, yayin da kwamishinan noma na jihar, Alhaji Muttaka Namadi ya sanya hannu a madadin gwamnatin Jigawa.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wani babban ci gaba a shirin gwamnatin sa na sauya fasalin harkar noma, tare da jaddada ƙudirin gwamnati na ƙarfafa ƙananan manoma ta hanyar shirye-shiryen tallafi masu ɗorewa.
Ya ce:
“A ƙarƙashin wannan shiri, za mu samar da kayan noma ga manoman shinkafa 20,000 domin gudanar da noman rani a faɗin jihar Jigawa.”
Gwamnan ya bayyana cewa an tsara haɗin gwiwar ne domin magance wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar manoma, musamman tsadar kayan noma da makamashin da ake amfani da shi wajen ban ruwa.
“A ƙarƙashin wannan shiri, gwamnatin Jigawa za ta bayar da tallafin kashi 30 cikin 100 na kayan noma ga manoman shinkafa 20,000 da ke noman rani a jihar.”
Ya ce wannan tallafi zai ƙarfafa manoma su koma gonaki tare da tabbatar da cewa harkar noma tana ci gaba da zama mai amfani da riba.
Haka kuma, Gwamna Namadi ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da rabon famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 6,000 ga manoman da ke cikin shirin, tare da tsarin biyan kuɗi cikin sauƙi na tsawon shekaru biyu.
A cewarsa, amfani da famfunan ruwa masu amfani da hasken rana zai rage wa manoma nauyin kashe kuɗi kan man fetur da makamashi, waɗanda suka zama babban ƙalubale ga noma a shekarun baya-bayan nan.
“Muna son manomanmu ba kawai su koma gona ba, har ma su samu riba mai ma’ana daga ayyukan nomansu. Shi ya sa muka yanke shawarar bayar da tallafin kayan noma tare da samar musu da kayan ban ruwa masu amfani da hasken rana.”
Gwamnan ya yaba wa kamfanin StarAgri West Africa Limited bisa haɗin gwiwar da ya yi da gwamnatin jihar, yana mai bayyana fatan cewa haɗin gwiwar zai buɗe sabon babi a ƙoƙarin Jigawa na bunƙasa noma da samar da wadataccen abinci.
Gwamna Namadi ya ƙara da cewa gwamnatin jihar a shirye take ta ci gaba da haɗin gwiwar tare da amfani da ƙwarewa da tallafin fasaha na kamfanin domin ƙara yawan amfanin gona ga ƙananan manoma.
“Mun ga jajircewar ku da sha’awar ku wajen tallafa wa ƙananan manoma, saboda haka muna shirye mu ci gaba da aiki tare da ku domin amfanin al’ummarmu,” in ji gwamnan.

