JGSG Ta Yi Jaje Ga AA RANO Kan Gobarar Da Ta Tashi a Gidan Mai na Kazaure
Kwamitin kula da harkokin man fetur na jihar (State Taskforce on Petroleum Products) ya bayyana gobarar da ta tashi a gidan mai na AA RANO da ke Kazaure a matsayin babban abin takaici.
Shugaban kwamitin, Kanal Muhammad Alhassan mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar jaje zuwa gidan man da abin ya shafa a garin Kazaure.
Ya ce tuni wata babbar tawagar gwamnati karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ta kai irin wannan ziyarar jaje dangane da lamarin.
Kanal Muhammad Alhassan ya bayyana gobarar a matsayin ƙaddara daga Allah, tare da yin kira ga masu gidajen mai da su kara daukar matakan tsaro da kiyaye dokokin aiki domin kaucewa irin wadannan hadurran gobara a nan gaba.
A nasa bangaren, Manajan gidan man, Malam Idris Yahuza Turaki, ya yaba wa Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa aiko da tawagogi biyu domin jajanta musu.
Ya ce wannan ziyara na nuna yadda gwamnan ke damuwa da halin da al’ummarsa ke ciki.
Manajan ya kuma bayyana cewa tuni aka fara aikin gyaran bangaren da gobarar ta shafa, tare da tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba za su koma gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba.
Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata ne wata tankar mai dauke da fiye da lita dubu sittin na PMS ta kama da wuta a gidan mai na AA RANO da ke Kazaure, sai dai babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

