GWAMNATIN JIGAWA ZA TA KARA KARFAFA HADIN GWIWA DA MASARAUTU DA SHUGABANNIN AL’UMMA DOMIN INGANTA TSARO
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da hada kai da masarautu da shugabannin al’umma domin kara inganta amincewa da hadin kai a harkokin tsaro.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bude taron gabatar da takardu da zaman tattaunawa na kwanaki biyu ga mahalarta Babban Kwas na 48 na Kwalejin Horas da Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya ta Armed Forces Command and Staff College da ke Jaji, wanda aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello Hall da ke Dutse.
Da yake wakiltar gwamnan, Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Aminu Usman, ya bayyana cewa ta hanyar shiga tsakani daga matakin kasa da tsarin ‘yan sanda na al’umma, Jihar Jigawa ta samu kwanciyar hankali mai kyau wanda ya bai wa gwamnati damar samun ci gaba a bangarorin ilimi, lafiya, noma da bunkasa tattalin arziki.
Ya bayyana taken rangadin nazarin da cewa, “Inganta Shigar Al’umma domin Tsaro da Wadata ta Kasa,” yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro, hukumomin farar hula da kuma al’ummomin gari wajen magance kalubalen tsaro na zamani.
“Taken da kuka zabo ya tabo daya daga cikin muhimman ginshikan zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a kasarmu a yau. Batu ne mai muhimmanci kuma ya dace da halin da kasar nan ke ciki. Shigar al’umma a matsayin masu ruwa da tsaki abu ne mai matukar muhimmanci. Kalubalen tsaro na zamani suna kara rikitarwa, kuma ba za a iya magance su da kokarin sojoji kadai ba. Dole ne a samu cikakken hadin kai tsakanin jami’an tsaro, hukumomin gwamnati da kuma al’ummomin da suke yi wa hidima,” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, tare da cewa ingantacciyar hulda da al’umma na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
“Mun kara karfafa hulda da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin gina amincewa, inganta tattara bayanan sirri da kuma bunkasa zaman lafiya tsakanin jama’a. Haka kuma muna tallafawa shiga tsakani daga matakin kasa a harkokin tsaro. Ta hanyar tsarin ‘yan sanda na al’umma, musayar bayanan sirri da hadin gwiwa da shugabannin gargajiya, mun ci gaba da karfafa amincewa tsakanin jama’a da hukumomin tsaro,” in ji gwamnan.
Ya ce sakamakon wadannan kokari, jihar ta samu kwanciyar hankali wanda ya bai wa gwamnati damar mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi ci gaba kamar ilimi, lafiya, noma da bunkasa tattalin arziki.
Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya yi maraba da mahalartan tare da sake tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na inganta rayuwar al’umma ta hanyar zuba jari a muhimman fannoni.
Ya ce kasancewar mahalartan a jihar abin alfahari ne kuma abin girmamawa, yana mai bayyana Kwalejin Armed Forces Command and Staff College da ke Jaji a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyin horas da shugabannin tsaro da dabarun yaki a Nijeriya da ma kasashen waje.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa irin wannan rangadin nazari yana bayar da dama wajen musayar ilimi, fahimtar tsarin shugabanci, gudanar da ci gaba, harkokin tsaro da hadin kai tsakanin hukumomi.
Ya kara da cewa gwamnatin Jigawa karkashin jagorancin Malam Umar A. Namadi na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi ilimi, lafiya, noma, gine-ginen more rayuwa, bunkasa matasa da tattalin arziki domin inganta rayuwar jama’a.
Shi ma shugaban tawagar mahalartan, Birgediya Janar B.O. Omopariola, ya bayyana Jigawa a matsayin jiha mai zaman lafiya, karamci da kuma ci gaba.
Ya ce an tsara rangadin ne domin bai wa mahalarta damar samun bayanai kai tsaye kan yadda gwamnatoci ke gudanar da harkokin tsaro da shigar al’umma a jihohin Nijeriya.
Birgediya Janar Omopariola ya bayyana cewa an zabo Jigawa domin gudanar da wannan atisaye saboda sunanta a matsayin daya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.
A yayin taron, kwamishinoni hudu sun gabatar da takardu, ciki har da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa Ahmed; Kwamishinan Ilimin Firamare, Dakta Lawan Yunusa Danzomo; Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Kimiyya da Fasaha, Farfesa Isah Yusuf Chamo; da Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa, Alhaji Muttaqa Namadi.
