: Ana Kira Shugabannin APC na Jihar Kano su Dakile Rikicin Siyasa a Tudun Wada/Doguwa
Ra’ayi
Daga: Muhammad Suleman Gama
Mai Sharhin Siyasa
Rana: 3 ga Mayu, 2026
Ana ci gaba da ganin gasa da fahimtar siyasa na kara tsananta a yankin Tudun Wada da Doguwa, musamman yayin da ake kokarin fitar da ‘yan takarar da za su fafata a zaben majalisar kasa.
Marubucin ya bayyana cewa, yadda ake zargin wasu na kirkirar sakamakon siyasa domin amfanar da ‘yan uwa ko na kusa, na kara janyo son kai da karkatar da siyasa daga turbar gaskiya.
Ya ce, makonni kadan da suka gabata sun yi hasashe kan halin da ake ciki, amma babu wani gyara da aka yi, lamarin da zai iya bai wa wasu ‘yan siyasa masu son zuciya damar juya al’amura yadda suke so.
A cewarsa, a jiya ne aka fara yada wani sabon bayani a kafafen sada zumunta da ke nuni da cewa an amince da wani tsohon jami’in tsaro mai ritaya ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilai, domin maye gurbin jagoran da aka dade ana yabawa bisa kwarewa da gaskiyarsa a fadin kasa.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ana zargin wata shugabar jam’iyya da kokarin goyon bayan wanda take da alaka ta kusa da shi, abin da ke nuna yadda siyasa ke kara tabarbarewa sakamakon son zuciya.
Sai dai wani jigo a yankin kuma tsohon kwamishina, Alhaji Nura Dankadai, ya musanta wannan zargi, inda ya tabbatar da cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa ne har yanzu dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada, kuma shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar APC a yankin.
Dankadai ya jaddada cewa Doguwa na ci gaba da kasancewa halastaccen dan takara bisa jajircewarsa da kuma kyakkyawan wakilcin da yake yi a majalisar kasa.
Ya kara da cewa al’ummar yankin ba za su mika wakilcinsu ga wanda ba shi da cikakken kwarewa ko karfin gudanar da ayyukan majalisa yadda ya kamata ba, domin martabar mazabar na da matukar muhimmanci a gare su.
A karshe, marubucin ya yi addu’ar Allah ya bai wa al’umma shiriya domin su fahimci jajircewar Hon. Alhassan Ado Doguwa a majalisar kasa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version