JIGAWA NA SHIRIN SAMUN ƘURI’U MASU YAWA GA TINUBU A ZABEN 2027 – GWAMNA NAMADI

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa burin jihar Jigawa a shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ba wai kawai ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓe ba ne, a’a, burin shi ne tabbatar da cewa ya samu ƙuri’u masu dimbin yawa daga jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi wata tawaga daga ƙungiyar siyasa ta Haske Bola Tinubu Organisation, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abba Atiku Abubakar, wadda ta kai masa ziyarar girmamawa a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
Malam Umar Namadi ya tabbatar wa ƙungiyar cikakken goyon bayan gwamnatinsa, tare da bayyana shirinsa na yin aiki kafada da kafada da mambobinta domin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na biyu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version